ABNA24 : Daga cikin wadanda za su iya gabatar da kansu a matsayin masu son tsayawa takarar shugabancin kasar da akwai masu rike da mukamai a banagrori uku na gwamnati, da mamabobin majalisar koli tsaron kasa, da majalisar kare maslahar tsarin musulunci. Sai kuma manajoji na cibiyar ilimin addinin musulunci ta Hauza, da sauran cibiyoyin gwamnati da masu zaman kansu, da kuma sojoji masu da mukaminsu ya kai janar da kuma shugabannin jami’o’i.
Daya daga cikin sharadin tsayawa takarar ya kunshi cewa; shekarun dan takara kada su yi kasa da 40, kuma kada su wuce 75.
Za a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar shawarar musulunci ne a ranar 18 ga watan Yuni.
342/